- Babban Lauya a Najeriya, Femi Falana, ya nemi gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan mutuwar Abba Kyari - Falana ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike kan mutuwar Abba Kyari duba da yadda yayi jinya a wani asibitin kudi da hakan na cin karo da ka'idar Hukumar Lafiya Wani babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Babban lauyan ya nemi gwamnatin da ta gaggauta aiwatar da bincike a kan ababen da suka dabaibaye jinya da kuma mutuwar marigayi Kyari.

Falana ya ce bukatar aiwatar da binciken ta zo ne duba da yadda aka yi jinyar marigayi Kyari a wani asibitin kudi sabanin yadda Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya shar'anta.


 A baya dai Mista Ehanire ya ce babu wani asibitin kudi a fadin kasar nan da aka yiwa lamunin duba lafiyar duk wani wanda cutar coronavirus ta harba kamar yadda jaridar NAIJA INSTA ta ruwaito.

Marigayi Mallam Abba Kyari da Femi Falana Marigayi Mallam Abba Kyari da Femi Falana Source:

UGC Lauya Femi ya ce wannan ce madogararsa ta neman gwamnati ta gudanar da binciken gaggawa kan mutuwar mai lura da al'amuran ma'aikatan fadar shugaban kasa da ajali ya katsewa hanzari. Lauyan ya ce duba lafiyar marigayi Mallam Kyari da aka yi a asibitin kudi ya sabawa ka'aidoji da kuma sharuddan da aka gindaya kan annobar cutar covid-19.